Wednesday, May 7
Shadow

Dokar-ta-ɓaci: Magoya bayan Fubara na gudanar da gangamin maida shi kan kujerarsa

Daruruwan magoya bayan dakatatcen gwamnan jihar River Siminalayi Fubara ne suka fito zanga-zanga a yau Talata, su na masu kira da a mayar da shi kan kujerar sa ta gwamna.

RFI ta rawaito cewa sun dai faro tattakin ne daga kan hanyar Aggrey, inda suke rike da alluna masu ɗauke da rubuce-rubucen cewa “muna tare da gwamna Sim Fubara”, “muna buƙatar a maido mana da gwamnanmu da muka zaɓa”, da dai sauransu.

Wannan ce dai gangami na baya-bayan nan da magoya bayan gwamnan suka gudanar, tun bayan dakatar da shi da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar 18 ga watan daya gaba.

Karanta Wannan  Kasar Equatorial Guinea ta hana sauke bidiyo saboda hana yada Bidiyoyin bàtsà na jami'in gwamnati guda 400 da aka ganshi yana làlàtà da matan mutane

A tattakin da su ke yi, sun riƙa rera wakoki da kade-kade da raye-raye tare da rera addu’o’in fatan a dawo da Fubara kan karagar sa ta mulkin jihar Rivers.

Dakatarwar dai ta shafi mataimakiyarsa Ngozi Odu da mambobin majalisar dokokin jihar, sakamakon taƙaddatar da ta yi zafi tsakanin ɓangaren zartarwa da kuma na dokoki.

Bayan dakatarwar da Tinubu ya yi wa gwamna Fubara, ya naɗa Vice Admiral Ibok-ete Ibas mai murabus, a matsayin kantoman rikon ƙwarya, lamarin da ya haifar da cecekuce a ƙasar na zargin an sama wa doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *