Wednesday, January 15
Shadow

Dole a samar da inshola ga masu haƙar ma’adanai – Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta tilastawa kamfanonin haƙar ma’adanai yin inshola ga ma’aikatan su, domin bayar kariya gare su idan wani haɗari ya faru.

Ministan ma’adanan ƙasar, Dele Alake, ya daga yanzu gwamnati ba za ta sake amincewa da lasisin duk wani kamfanin haƙar ma’adanai da bai nuna ƙwaƙwarar shaidar cika ƙa’idojin gudanar da aiki ba.

Ministan ya na magana ne lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya da jaje a jihar Neja, inda ƙasa ta rufta da masu haƙar ma’adanai a ƙauyen Galkogo na ƙaramar hukumar Shiroro.

Ya ce gwamnati za ta tabbatar da bin duk hanyar da ta dace domin kare afkuwar irin wannan matsala a nan gaba, dmin haka ta faraɓullo da irin wannan mataki.

Karanta Wannan  Za'a yi zanga-zangar yunwa da rashin abinci a Najeriya

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja a Najeriya (NSEMA) ta ce kimanin mutum 30 ne ake fargabar sun mutu sakamakon zaftarewar kasar da ta auku a wani wurin hakar ma’adinai, a ranar Litinin.

Hukumomin jihar sun ce ana ci gaba da aikin ceton mutanen da ƙasar ta rufta da su, duk da cewa ana samun koma baya a aikin saboda ruwan sama da kuma ƙalubalen tsaro a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *