
Daga Datti Assalafiy
Lokacin da Allah Madaukakin Sarki ya zare ran babban Malamin Tauhidi na Afirka Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi, wadannan manyan Malamai wato Sheikh Dr Ibrahim Disina da Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum suna samun labari suka taho gidan Malam.
Sannan sukace a tattaro musu list na mutanen da suke bin Malam bashi zasu biya daga aljihunsu, basa bukatar a biya bashin da kudin Malam.
Wallahi wadannan Malamai basu bari an yiwa Malam Sallar jana’iza ba sai da suka biya duk bashin da ake binsa, kana zuwa da shaida da ta tabbatar kana bin Malam bashi nan take suke biya komin yawan kudin.
Lokacin da jinyar ajali ta kama Malam zai yafi Kasar Egypt jinya, ya fara neman visa, sai daga baya aka canza shawara a wuce Kasar Indiya kawai, kuma haka akayi, to daga baya visa na Egypt ta fito, suma sun aiko da lissafin kudi a matsayin bashi da suke bin Malam, kuma wadannan Malamai sun biya.
Kowa ya sani Malam yana da dunbin dukiyar da za’a biya masa bashin da ake binsa, amma wadannan Malamai sukace kar a biya da kudin Malam su zasu biya da kudinsu, idan ba cikakken masoyinka na gaskiya ba babu wanda zai maka haka.
A rayuwa baka fahimtar waye cikakken masoyinka sai ranar da ka fada cikin jarrabawa ta rayuwa, ko kuma sai bayan ka mutu a lokacin ne masoyanka na gaskiya zasu biya maka bashin da ake binka, sannan su kula da iyalanka.
Muna rokon Allah Ya saka musu da Aljannah.