Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan ci gaban yankunan kasarnan, Abubakar Momo ta bayyana cewa dolene sai Gwamnatin ta dauki matakan shan wahala kamin a samu warware matsalolin kasarnan.
Ministan yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana nufin Najeriya da Alherine.
Ya bayyana hakane a Akure wajan kaddamar da rabon kayan tallafi ga jihohin Yankin Naija Delta.
Ministan yace kwanannan za’a ga amfanin gyare-gyaren da gwammatin Tinubun ke kawowa.
Yace idan dai ana son kawo gyara sai an dauki matakan shan wahala tukuna.