Monday, December 9
Shadow

Dole sai mun dauki matakai na shan wahala kamin a samu gyara a kasarnan>>Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu

Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan ci gaban yankunan kasarnan, Abubakar Momo ta bayyana cewa dolene sai Gwamnatin ta dauki matakan shan wahala kamin a samu warware matsalolin kasarnan.

Ministan yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana nufin Najeriya da Alherine.

Ya bayyana hakane a Akure wajan kaddamar da rabon kayan tallafi ga jihohin Yankin Naija Delta.

Ministan yace kwanannan za’a ga amfanin gyare-gyaren da gwammatin Tinubun ke kawowa.

Yace idan dai ana son kawo gyara sai an dauki matakan shan wahala tukuna.

Karanta Wannan  An kashe mutane 4, 30 sun jikkata bayan da wani dan bindiga dadi ya budewa wuta akan mutane a makaranta a kasar Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *