Donald Trump ya sha rantsuwa a matsayin shugaban Amurka na 47, bayan nasarar da ya yi a zaɓen shugaban ƙasar na 2024.
An rantsar da Donald Trump ne a cikin ginin Majalisar Dokokin ƙasar na Capitol, karon farko a cikin shekaru.
Gabanin Trump, an rantsar da mataimakinsa, kuma tsohon mai sukarsa, JD Vance.
Jim kaɗan bayan shan ranstuwa, Trump ya sanar da wasu tsauraran matakai da zai ɗauka, musamman a ɓangaren tsaron iyaka da kuma rage kwararar baƙi zuwa ƙasar.
Wani abin kuma shi ne yadda Trump ya riƙa sukar magabacinsa, Joe Biden, a gabansa, jim kaɗan bayan shan rantsuwa.
Donald Trump ya dawo kan mulki ne bisa alƙawarin kawo tsauraran sauye-sauye waɗanda suka sha bamban da na Biden.
A jawabinsa na farko, Trump ya ce ”Sabon babin ci gaban Amurka zai fara ne daga yau”.
”Daga yau, ƙasarmu za ta fara samun ci gaba kuma za a mutunta ta a duniya”
“Zan sanya muradun Amurka a gaban komai.”
- karo da juna20 Nuwamba 2024
Abubuwan da Trump zai yi a ranar farko bayan shan ranstuwa
Shige da fice:
- Trump zai ayyana dokar ta-ɓaci a kan iyakar ƙasar don aikewa da ƙarin sojoji da ma’aikata
- Zai umarci jami’ai su ci gaba da ginin katangar kan iyakar Amurka da Mexico
- Shugaban na son soke izinin zama ɗan ƙasa ga ƴaƴan baƙin haure da suka shiga Amurka ba bisa ƙa’ida ba
- Yana shirin mayar da tsarin da ake kira ‘Remain-in-Mexico’, wanda ke buƙatar baƙi su yi zaman jira a Mexico yayin da suka miƙa buƙatar neman mafaka.
Tattalin Arziki:
- Trump na shirin kafa dokar ta-baci a ɓangaren makamashi na ƙasar, wanda a cewarsa zai bai wa ƙasar damar samar da albarkatun ƙasa da kuma samar da ayyukan yi.
- Har ila yau, yana son “kawo ƙarshen batun tilasta aiki da motoci masu amfani da lantarki” da kuma ƙoƙarin da ake yi na daƙile zaɓin masu amfani kayayyaki, a cewar gwamnatinsa.
- A cewar jaridar Wall Street, Trump na shirin bai wa gwamnati umarnin sake fasalin alaƙar kasuwancin tsakanin Amurka da China – amma bai shirya sanya sabbin haraji ba.
Batutuwan da suka shafi jinsi:
- Yana shirin aiwatar da dokar da za ta kawo ƙarshen tsarin DEI, wanda ke tabbatar da daidaito kan batun jinsi a cikin gwamnatin tarayya”
- Wani umarni na zartarwa zai “bayyana cewa manufar Amurka ce ta tabbatar da jinsi biyu kaɗai- namiji da mace” waɗanda ba za a iya sauya su ba.