Monday, December 16
Shadow

DSS ta kama shugaban ƙungiyar ƙwadago Joe Ajaero

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero.

Kungiyar ta NLC ta bayyana a shafin sada zumuntarta na X cewa an kama shugaban nasu ne a yau, Litinin da safe a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Ƙungiyar ta NLC ta ce “har yanzu ana ci gaba da cin zarafin ma’aikatan Najeriya yayin da shugabanmu Joe Ajaero ya shiga hannun jami’an DSS da safiyar yau.”

“Jami’an sun kama shi ne akan hanyarsa ta zuwa taron ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Birtaniya.”

NLC ta ce yanzu haka ana tsare da shugaban a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro NSA.

Karanta Wannan  Da dumi'dumi: 'Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda da Dan Banga A Jihar Sokoto

A baya dai, shugaban NLC ɗin ya mutunta gayyatar da ƴansanda suka yi masa kan zarginsa da hannu a tallafawa ayyukian ta’addanci, da kuma cin amanar ƙasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *