
Dubban mutane ne suka taru a dandalin St Peter a Asabar din nan domin jana’izar Paparoma Francis
Shugabanni da dama na duniya ne suka halarci jana’izar ciki har da shugaban Amurka Donald Trump da na Ukraine Volodymyr Zelensky, wanda ake saran za su gana a can, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na AFP ya rawaito.