Tuesday, May 19
Shadow

EFCC zata binciki tsohon shugaban Kamfanin mai na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar yaki da Rashawa da cin hanci, EFCC ta sha Alwashin biciken tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPL, Mele Kolo Kyari.

Hakan ya biyo bayan korafin da wasu lauyoyi da kungiyoyin kare hakkin al’umma suka mikawa EFCC din.

Wadannan kungiyoyi sun yi zanga-zanga ne a ofishin EFCC suna duka zargi Kyari da aikata rashawa da cin hanci da kuma yiwa tattalin arziki Najeriya zagon kasa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale ya karbi takardun korafin kungiyoyin a madadin shugaban hukumar inda yace zasu duba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Kwanaki 2 bayan kammala dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya, Har yanzu akwai sauran shinkafar bata kare ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *