
A wata hira da ya yi da gidan radiyon jakadiya ɗan siyasar ya bayyana irin salon siyasar madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da cewa ya butulce wa duk waɗanda suka taimake shi a siyasa, saboda haka canza shekar da ’yan majalissar jam’iyyarsa suka yi alama ce ta rasin ingantaccen shugabanci na jagoran na Jam’iyyar NNPP.