Bankin Duniya ya baiwa Gwamnatin Najeriya shawarar cewa ta ci gaba da tsarin da take kai a yanzu na tsawon shekaru 10 ko 15 idan tana son samun ci gaba ba a Afrika kadai ba harma da Duniya baki daya.
Wakilin bankin Duniyar, Indermit Gill ne ya bayyana haka a wajan wani taron tattalin arziki da ya gudana a Abuja.
Ya kawo tsare-tsaren gwamnati na cire tallafin dala da mai da saransu wanda ya ce ya kamata a ci gaba da aikatasu dan samun ci gaba me dorewa.
Saidai a yayin da yake jawabin, an rika masa ehon ba’a son wannan shawara tasu ta bankin Duniya amma du da haka yace ba lallai ne a yadda da abinda yake fada ba amma gaskiyace.