Friday, December 5
Shadow

Duk da Dangote na kai musu man da suka saya da tankokin Motocinsa Kyauta, Har yanzu gidajen man fetur basu rage farashin ma nasu ba

Rahotanni sun ce duk da Dangote na daukar man fetur din da gidajen mai suka siya da tankokin motocin sa yana kai musu kyauta.

Har yanzu gidajen man basu rage farashin man fetur din da suke sayarwa ba.

An yi tsammanin tunda babu kudin dakon mai da gidajen man fetur din ke biya, Dangote na kai musu kyauta da tankokinsa, farashin man da suke sayarwa zai sakko kasa.

Saidai hakan bata faru ba inda hadda gidan man MRS wanda shine yafi kusa da Dangote wanda suka yi hadaka, shima a wasu wajajen farashin litarsa na kaiwa har Naija 875, kamar yanda jaridar Punchng ta ruwaito bayan yin zagaye ta ga yanda ake sayar da mai a gidajen man.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon me dokar bacci: An kama Dansanda na satar Wayar wutar Lantarki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *