
Da yawan ‘yan Arewa ne suke sukar ziyarar da dan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai jihohin Arewa inda ya raba kayan abincin buda baki.
Wasu dai na ganin wannan rabon abincin da yayi ma cin fuskane kamar ya mayar da mutane mabarata ne ko mayunwata.
Daya daga cikin wadanda suka soki dan shugaban kasar akwai dan gwamnan Bauchi, Shamsuddeen Bala Mohammed
Shamsuddeen ya nemi dan shugaban kasar maimakon raba abinci a hannu, ya karfafu matasa da jari ko ayyukan yi zai fi inda ya bayyana cewa irin wannan rabon abincin da yake alamace dake nuna cewa mahaifinsa ya gaza.
Hakanan a kafafen sada zumunta da yawa ma an samu masu sukar dan shugaban kasar.
Da yawa sun bayyana ra’ayi irin na dan Gwamnan Bauchi inda suke ganin kawowa mutane musamman matasa abubuwan ci gaba shi yafi fiye da raba musu abinci da zasu cinye yanzu su sake neman wani an jima.