Monday, April 21
Shadow

Yanzu-Yanzu: Dangote yace zai daina sayarwa da Najeriya man fetur

Rahotonni sun bayyana cewa, Attajirin dan kasuwa Aliko Dangote zai daina sayarwa da Najeriya man fetur.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa Dangote na son daukar wannan mataki ne biyo bayan kasa cimma matsaya akan ci gaba da cinikin man fetur din da kudin Naira maimakon dalar Amurka.

Saidai majiyar tace matatar man zata ci gaba da fitar da man fetur din zuwa kasashen waje dan kuwa dama daga kasashen wajen take siyo danyan man da take tacewa.

Matatar Dangote na sayarwa da Najeriya man fetur din data tace ne da Naira saboda a kudin Naira take sayen danyen man fetur da take saya daga hannun gwamnati.

Karanta Wannan  Ba gaskiya bane Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu basa aiki>>Gwamnatin Jihar Bauchi ta mayarwa da Bankin Duniya martani

Saidai wannan yarjejeniyar a yanzu ta kare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *