
Rahotanni sun bayyana cewa, babban Bankin Najeriya, CBN ya bayar da dala Biliyan $1.259 dan a shigo da man fetur da sauran wasu abubuwa masu alaka dashi zuwa cikin Najeriya.
An saki kudadenne a watanni 3 na farko na shekarar 2025 da muke ciki.
Hakan na zuwane yayin da rikici ke ci gaba da ruruwa tsakanin ‘yan kasuwar da Dangote inda yake cewa a hanasu shigo da man fetur daga kasashen waje su kuma suna cewa basu yadda ba saboda ba zai iya wadata Najeriya da man fetur din da yake samarwa ba.
Sannan suna zargin Dangoten da kokarin mamaye harkar man gaba daya a Najeriya.