Friday, December 26
Shadow

Duk da ni dan APC ne, bana goyon bayan Tinubu ya zarce a 2027 saboda ‘yan Najeriya na cikin wahala>>Inji Sanata Ali Ndume

Sanata Ali Ndume wanda ya fito daga jihar Borno ya bayyana cewa baya cikin ‘yan jam’iyyar APC da suke neman shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zarce.

Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.

Sanata Ali Ndume yace dalilinsa kuwa shine lamura sun kazance a kasarnan inda farashin kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabo, ga matsalar tsaro kuma rayuwa ta wa talaka tsanani.

Yace ‘yan Najeriya basa hangen wani abin ci gaba a gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu.

Yace kuma kada shugaba Tinubu ya rudu da maganar Gwamnonin APC da suka ce suna goyon bayansa, ya tuna cewa, Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan gwamnoni 22 suka goyi bayansa amma duk da haka ya fadi zabe.

Karanta Wannan  Ba kamar yanda ake cewa mun Kàshè 'yan sa kai da yawa ba a Zamfara, Guda biyu ne kawai suka mùtù bayan jirgin saman mu yayi kuskuren jefa musu Bàm da tunanin cewa 'yan Bìndìgà ne>>Hukumar Sojojin Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *