Thursday, October 3
Shadow

Akwai yiyuwar shugaba Tinubu yayiwa majalisar zartarwa garambawul

Akwai yiyuwar Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu zai canja wasu ministoci a majalisarsa ta zartaswa.

Hakan wani mataki ne na cire ministocin da basa tabuka wani abin azo a gani.

Shugaban dai ya jima yana fuskantar matsi akan ya canja ministocin da basa yin aikinsu yanda ya kamata.

A shekarar da ta gabata ne dai shugaban kasar ya kafa wani tsari na auna kokarin ministocin inda yayi gargadin duk wanda ba ya kokari za’a koreshi daga aiki.

Karanta Wannan  IMF ya nemi Tinubu ya tausaya wa talakawan Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *