
Rahotanni sun ce har yanzu gidajen man fetur na sayar da man a farashi me tsada duk da rage farashin da matatar man fetur ta Dangote ta yi.
A makon daya gabata ne Matatar man ta sanar da rage farashin daga Naita 865 zuwa naira 820 akan kowace lita musamman tace saboda tankokin man ta 1000 zasu fara jigilar man zuwa gidajen mai kyauta.
Saidai binciken da jaridar Punchng ta yi yace har yanzu a jihohin Legas da Ogun da sauran wasu jihohi gidajen man basu fara sayar da man a sabon farashi ba.