
Sufeto Janar na ‘Yansandan Najeriya Olukayode Egbetokun ya ce sun aiwatar da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na janye dakarunsu daga gadin ɗaiɗaikun mutane da ake kira VIP.
Yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, IG Egbetokun ya ce zuwa yanzu sun janye dakaru 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Najeriya.
“Wannan karon za muj aiwatar da umarnin da kyau saboda umarnin shugaban ƙasa ne,” in ji shi.
“Babu wani gwamna, ko minista, ko abokaina da za su kira su takura min saboda sun san cewa umarnin shugaban ƙasa ne. Ina da tabbacin ba za su uzura wa kwamashinonin ‘yansanda ba ma.”
Ya ƙara da cewa za su tura jami’an da aka janye zuwa “wuraren da aka fi buƙatarsu, musamman a wannan lokaci mai muhimmanci”.