
Tauraruwar fina-finan Hausa, Kilishi ta bayyana rashin jin dadinta kan kalaman da ake yi musamman akan taurarin fina-finan mata da cewa basa son zaman aure.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyon ta dake yawo a kafafen sadarwa inda tace Aure mutuwa da haihuwa duk na Allah ne.
Tace wanda kuma bai yadda ba sai yawa kansa Arziki.