
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa masu tambayar ya aka yi da kudin tallafin man fetur su zo jihar Nasarawa su ga yanda aka yi dasu.
Ya bayyana hakane a yayin ziyarar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai jihar Nasarawa ta kwanaki daya inda ya samu rakiyar manyan ma’aikatan Gwamnati ciki hadda Gwamnonin APC da dama.
Gwamnan yace manya-manyan canje-canjen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kawo wa Najeriya sune cire tallafin Man fetur sai kuma cire tallafin dala.
Ya bayyana cewa kuma duka an shaida irin ci gaban da hakan ya kawo musamman su a jiharsu ta Nasarawan.