
Dala 10 ba za ta siya maka abinci a Amurka ba, amma $1 za ta baka abinci a Najeriya – Tope Fasua, in ji hadimin Tinubu
Dr. Tope Fasua, Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, ya bayyana rikice-rikicen da ke tattare da auna talauci, yayin da yake kare darajar Naira a cikin gida, inda ya kwatanta tsadar rayuwa a Najeriya da ta Amurka.
Yayin da yake magana a cikin shirin MicOnPodcast tare da Seun Okinbaloye, Fasua ya bayyana cewa mutane da dama a Najeriya ba su fahimci ma’anar talauci mai fuskoki da dama ba, wanda ake yawan amfani da shi a cikin kididdigar talauci ta duniya.
“Wasu mutane ba su fahimci ma’anar talauci mai fuskoki da dama ba,” in ji shi. “Suna ganin kamar yana da muni fiye da talauci na rashin abinci. Abin da ake nufi da talauci mai fuskoki da dama shi ne, watakila makarantar da ‘ya’yanka ke zuwa tana da nisa da kai, ko asibiti, sai a sanya ka a jerin masu talauci mai fuskoki da dama.”
Ya ci gaba da bayani cewa duk da tsadar musayar dala da naira, ikon siyan kaya da Naira a Najeriya yana da tasiri idan aka kwatanta da rayuwa a ƙasashen waje.
“Dala ɗaya na Naira 1,500 – wannan babbar kudi ce ga mutane da dama a Najeriya. Dala 10 ba zai siya maka abincin rana a kowanne wuri a Amurka ba. Wani lokaci sai ka kashe aƙalla dala 20, wato Naira 30,000 a Najeriya,” in ji Fasua.