
Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Rivers, Tony Okocha ya baiwa gwamnan jihar, Siminalayi Fubara zabin ko dai ya ajiye mukaminsa salin Alin ko kuma a tsigeshi.
Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai ranar Litinin a babban birnin na jihar watau Fatakwal.
Ya bayyan gayyatar da Fubara yawa ‘yan majalisar jihar da cewa ta mugunta ce.
Okocha yace sun baiwa Gwamna Fubara awanni 48 ya sauka ko a tsigeshi.