
Hukumar ‘yansandan babban birnin tarayya, Abuja ta gargadi ‘yansandan cewa duka da zagin wanda ake zargi baya cikin aikinsu.
An bayyana musu hakane a yayin wani taron karawa juna Sani da aka yi.
Akan samu rahotannin jikkata masu laifi ko wanda ake zargi da ‘yansanda suka kama daga lokaci zuwa Lokaci.