
Wasu masu ruwa da tsaki a jami’iyyar PDP sun koka da cewa Jam’iyyar ta kama hanyar rugujewa inda suka yi kira ga ‘yan Jam’iyyar a dukkan fadin Najeriya da su tashi tsaye dan cetota.
Sun bayyana hakane a wajan wani taro da ya gudana a Abuja ta bakin wakilinsu, Obinna Nwachukwu.
Ya bayyana cewa, akwai bukatar ‘yan Jam’iyyar daga kowane sashe na kasarnan su fito dan yunkurin hanata durkushewa.
Yace lokaci yayi da zasu daina rungume hannu suna ganin yanda wasu ‘yan Jam’iyyar suke mata zagon kasa, wasu ma daga ciki har mukami aka basu a Jam’iyya me mulki ta APC suna ayyuka da kalamai na kokarin ruguza PDP.
Yace Jam’iyyar PDP itace wadda talaka ya dogara da ita a matsayin Jam’iyyar adawa wadda zata kalubalanci Jam’iyyar APC me mulki da kwatowa talaka ‘yancinsa.