Saturday, March 15
Shadow

EFCC ta kama tsohon Gwamnan Akwa-Ibom bisa zargin satar Naira Biliyan 700

Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kama tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Udom Emmanuel bisa zargin satar Naira Biliyan 700 a yayin mulkinsa.

Tsohon Gwamnan ya shiga komar EFCC ne a yayin da yace ofishin hukumar dan amsa gayyatar da suka masa kan zargin Rashawa da cin hanci.

Wata kungiyar dake yaki da Rashawa da cin hanci me suna (NACAT) ce ta shigar da korafi akan tsohon gwamnan.

Kungiyar ta yi korafin cewa, tsohon gwamnan ya karbi Naira Tiriliyan 3 a zamanin da yayi mulki tsakanin shekarun 2015 da 2023 daga gwamnatin tarayya.

Saidai ya tafi ya bar jiharsa da bashin Naira Biliyan 500 sannan akwai ayyukan da ake yi na jihar na Naira Biliyan 300 wanda bai biya ba sanan ana zargin yayi sama da fadi da naira Biliyan 700.

Karanta Wannan  Yarbawa sunce basu yadda da kotunan shari'ar musulunci a jihohinsu ba

Zuwa yanzu dai hukumar EFCC bata ce uffan kan wannan lamari ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *