Thursday, January 9
Shadow

EFCC ta kori ma’aikatanta 27 saboda ‘zambatar’ mutane

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta kori ma’aikatanta 27 a shekarar 2024 saboda zargin aikata zamba da sauran laifuka.

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa shugaban hukumar Ola Olukoyede ne ya amince da matakin.

“Duk wani zargi da aka yi wa wani ma’aikacin hukumar, sai an bincika shi, ciki har da na dala 400,000 da ake yi wa wani ma’aikaci da ba a gano shi ba zuwa yanzu,” a cewar sanarwar.

Ya ƙara da cewa EFCC “na sane da ayyukan sojan gona da ɓata sunan da wasu ke yi da ta hanyar amfani da sunan shugaba [Olukoyede] domin zambatar manyan mutanen da ake zargi”, wanda shi ma ake kan bincikawa.

Karanta Wannan  Hotuna: Kalli Yanda mata ke neman maza suna biyansu suna lalata dasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *