Tuesday, May 19
Shadow

Ruwa kamar da bakin ƙwarya ya janyo ambaliya a Makka

Matsanancin yanayi ya haifar da ambaliyar ruwa a wasu sassan ƙasar Saudiyya.

Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya mamaye hanyoyi a cikin garin Makka.

Haka kuma an ga yadda wasu maza suka riƙe da hannu domin ceto yaran da suka maƙale sanadin ambliyar ruwan a unguwar Al-Awali.

Sai da aka soke jigilar wasu jiragen sama a birnin Jeddah, inda aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya janyo hukumomin Saudiyya suka rufe makarantu a daukacin ƙasar.

Karanta Wannan  Na Allah basa karewa: Kalli Bidiyon yanda dan Sahu ya mayar da Naira Miliyan 4 da wani dan kasuwa ya manta a cikin kekensa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *