
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.
Wasu makusantan Sanatan ne suka tabbatar wa BBC sakin nasa, kuma yanzu haka yana gidansa na Abuja.
A ranar Litinin ne hukumar ta tsare shi a Abuja, bayan amsa gayyata kan zarge-zargen fitar da maƙudan kuɗaɗe da suka kai Naira biliyan 189.
Kamun da aka yi masa ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, musamman tsakanin ƴan hamayya, waɗanda ke zargin hakan na da alaƙa da rawar da yake takawa a tafiyar ƴan jama’iyyar haɗaka ta ADC.