Sunday, December 14
Shadow

EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, ta tsare tsohon ministan ƙwadago kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Chris Ngige.

Mai magana da yawun Ngige, Fred Chukwuelobe, ya tabbatar da tsare shi da safiyar ranar Alhamis, bayan wasu rahotanni da aka yaɗa cewa an sace shi.

Chukwuelobe ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “Ngige yana tare da EFCC. Ba a sace shi ba.”

Har zuwa yanzu, EFCC ba ta bayyana dalilin tsare Ngige ba amma kuma ana sa ran hukumar za ta fitar da cikakken sanarwa kan tsare shi da binciken da take yi a kansa.

Ngige ya zama mutum na biyu daga cikin tsoffin ministocin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da aka tsare a kwanan nan. Kafin shi, an fara tsare tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, wanda shima yake hannun EFCC.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo Da Duminsa: An Sàcè kanin Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare>>Inji Mahdi Shehu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *