
Wani fasto me suna Stephen Akintayo ya nemi mutane su biyashi dala 18,000 dan ya koya musu yanda zasu inganta rayuwarsu.
Lamarin ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta saboda kudin a Naira sun kai kwatankwacin Naira Miliyan 30.
Faston yace da farko mutum zai fara bayar da Naira Miliyan 2.5 kamin daga baya sauran kudin ya rika badasu a hankali har zuwa karshen shekara.
Saidai hukumar EFCC ta bakin kakakinta, Dele Oyewale ta gargadi mutane su yi hattara da irin wannan yaudarar.
Hakanan shima Mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya gargadi mutane da cewa su yi hattara da inda suke saka kudinsu.