
Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar yaki da Rashawa da cin hanci, EFCC ta sha Alwashin biciken tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPL, Mele Kolo Kyari.
Hakan ya biyo bayan korafin da wasu lauyoyi da kungiyoyin kare hakkin al’umma suka mikawa EFCC din.
Wadannan kungiyoyi sun yi zanga-zanga ne a ofishin EFCC suna duka zargi Kyari da aikata rashawa da cin hanci da kuma yiwa tattalin arziki Najeriya zagon kasa.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale ya karbi takardun korafin kungiyoyin a madadin shugaban hukumar inda yace zasu duba.