Friday, September 4
Shadow

El-Rufai bai koya min siyasa ba, ba me gidanane a siyasa ba>>Inji Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Sanata Uba Sani ya musanta ikirarin cewa, Tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai uban gidanda ne a siyasance kuma shine ya koya masa soyasa.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda aka tambayeshi me zai ce game da ikirarin El-Rufai na cewa shine ya koya masa siyasa?

Gwamna Uba Sani yace baya son mayar da martani akan wani mutum daya dan hankalinsa na kan jihar Kaduna.

Yace amma Shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu da tsohon lauya, marigayi Chief Gani Fawehinmi sune iyayensa a siyasa sune suka koya masa siyasa.

Karanta Wannan  Hukumomin sojin Amurka sun sace kudin da aka ware dan ciyar da sojojin kasar Abinci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *