Friday, December 5
Shadow

Facebook da Instagram sun kulle shafin mawakin Najeriya, Edris Abdulkarim saboda yiwa Trump waka

Shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram sun kulle shafin mawakin Najeriya, Edris Abdulkarim saboda wakar da yawa shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Idris yayi wakar ne akan harin da aka ce Trump din zai kawo Najeriya.

Sannan ya bayyana irin matsalolin tsaron da Najeriya ke fama dasu.

Ya kuma bayyana irin satar kudin da ‘yan siyasa ke yi da rashawa da cin hanci yayin da Talakawa ke fama da matsalar tsaro da Talauci.

Saidai bincike ya nuna cewa tuni an kulle shafinsa saboda wannan wakar.

Karanta Wannan  Ji Farashin da Dangote zai sayar da man fetur dinsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *