Saturday, June 27
Shadow

Dalibai Kiristoci na Jami’o’in Federal University Kashere, Gombe da BUK Kano sun koka da cewa akwai masallatai da yawa a wadannan jami’o’in amma an hanasu gina coci ko guda daya

Daliban jami’o’in Federal University Kashere, Gombe dana jami’ar BUK, Kano Kiristoci sun koka da cewa, akwai masallatai da yawa a wadannan jami’o’in amma an hanasu gina coci ko guda daya.

Daya daga cikin daliban na Kashere ne ya fito yake zanga-zanga shi kadai inda yace suna bukatar Coci a jami’ar.

Wani kirista ta bayyana cewa abin haushin shine jihar Gombe da yawan musulmai da kirista daidai suke watau 50/50 amma irin wannan abin na faruwa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Babban Kuskuren da 'yan Darika zasu yi shine su taba Sheikh Lawal Triumph, Inji Malam, Yaje sun hmga ba zasu iya fadan Littafi ba shine suke son tada zaune tsaye

Wannan zanga-zanga da dalibin yayi tasa shima wani dalibin jami’ar BUK Kano ya bayyana cewa suna hakan take, akwai masallatai a BUK amma su ba’a basu damar gina coci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *