
Fadar Shugaban kasa ta bukaci Kwankwaso ya bayar da hakuri ga Tinubu, ya janye maganganunsa kan Gwamnati
Daga Ayau News
Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi, ya bukaci tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ya bada hakuri ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kalaman da ya yi game da gwamnati.
Ayau News ta ruwaito Umahi ya ce maganganun Kwankwaso na zargin gwamnati tana fifita kudu ba su dace ba. Ya bukace shi da ya janye su domin gujewa rarrabuwar kawuna a kasa.
Kwankwaso ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna fifiko kan yankin kudu, yana cewa an bar Arewa a baya wajen ayyukan cigaba.
— A Yau News
Me zaku ce?