Wednesday, April 1
Shadow

Fadar shugaban kasa, ta sai Dutsen Guga guda biyu akan Naira Miliyan 10

Rahotanni daga fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sun bayyana cewa, Fadar ta sayi Dutsen guga guda biyu akan Naira Miliyan 10.

Watau kowanne dutsen guga an sayeshi akan Naira Miliyan 5 kenan.

An saiwa ofishin mataimakin shugaban kasa, wannan Dutsen gugar ne, kamar yanda kafar dake saka ido akan yanda ake kashe kudin Gwamnati, Govspend ta ruwaito.

Lamarin dai ya baiwa mutane mamaki.

Karanta Wannan  Bayanan Sirri da suka fito na karawa Dogarin shugaba Tinubu Mukami sun jawo cece-kuce sosai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *