
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya kuma shugaban hukumar Hizba ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce duk da cewa dukkannin ranaku da dararen watan Ramadan na da falala amma kwanaki 10 na ƙarshen watan sun fita daban.
“Goman ƙarshe na da wasu abubuwa guda uku masu muhimmancin kuma wannan ne ma ya sa ake fifita goman ƙarshen a kan goman farko da na tsakiya.” In ji Sheikh Daurawa.
- Allah ya yi rantsuwa da darare 10: Na farko dai Allah ya yi rantsuwa da su inda a cikin Alƙur’ani ya ce Wal Fajr, Wa Layalil A’shar. Malamai sun ce wannan na nuni da kwanakin ƙarshe na Ramadan ko kuma goman farko na watan Zulhijja.
- Daren Laylatul Qadr ya faɗo a goman ƙarshe: Abu na biyu a cikin wannan watan akwai daren Laylatul Qadr. Idan mutum ya yi dace a daren 21 ko 23 ko 25 ko 27 ko 29 to a wurin Allah zai kasance kamar wanda ya shekara 84 da watan huɗu yana bauta domin shi ne wata 1000 saboda haka bai kamata mu yi wasa ba da wannan dare.
- I’tikafi ya faɗo a goman ƙarshe: Abu na uku shi ne a waɗannan kwanakin goma ne ake shiga I’tikafi inda mutum ke tarewa a wani masallaci domin gana wa da mahallinsa. Ana so mutum ya yi I’tikafi kuma yana farawa ne daga kwana ɗaya har zuwa kwana 10.
- Shehun Malamin ya ƙara da cewa “Nana Aisha, matar manzon Allah SAW ta ce “idan goman ƙarshe ya zo, annabi SAW yana abubuwa guda uku” kamar haka:
- Ƙara yawan ibada
- Raya dararen 10
- Tashin iyalai su ma su yi ibada
- Sheikh Daurawa ya kuma ce “Nana Aisha ta ƙara da cewa ta tambayi annabi SAW cewa idan na da dace da Laylatul Qadr me zan roƙa? Sai ya ce min “ki ce Allah kai me rangwame ne ka yi min rangwame. Allah kai me afuwa ne ka yi min afuwa..”