
A yayin da aka fara shigo da shinkafa daga kasashen waje, misali kasar Benin zuwa Najeriya, farashin buhun shinkafa musamman a kauyuka ya koma Naira dubu 58,000.
Kungiyar S&P Global ce ta fitar da wadannan bayanai inda tace farashin shinkafar a yankin Afrika ta yamma yayi faduwar da ba’a taba ganin irin ta ba tun shekaru 2 da suka gabata.
Hakan na da alaka da cire harajin fitar da shinkafa zuwa kasashen waje da kasar India ta yi, kamar yanda rahoton ya nuna.
Farashin shinkafar ya sauka daga Naira Dubu 80 zuwa Naira dubu 58 kan kowane buhu.
Rahoton ya kara da cewa, kasar India ta ta kawo shinkafa me yawa yankin na Afrika maso yamma.