
Juna-biyun da na ke ɗauke da shi ba shi da alaƙa da wani gwamna – Jaruma Nengi
Nengi Hampson, tsohuwar jaruma a shirin fim na gasar Big Brother Naija (BBNaija), ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sadarwa cewa tana dauke da juna biyu da wani gwamna a Najeriya ya yi mata.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa rahotannin farko sun yi ikirarin cewa jarumar mai shekara 27 ta haifi jariri ga wani gwamna mai shekara 65 kuma har ta zama matarsa ta biyar.
A wani rubutu da ta wallafa kwanan nan a shafin X, Nengi ta bayyana takaicinta game da wannan jita-jita, tana mai cewa da ta sani ma da ta kau da kai daga jita-jitar.
Sai dai ta ce dole ta yi magana saboda abin ya shafi mutanen da ta ke girmamawa sosai.
Jarumar ta jaddada cewa ba za ta bari wannan jita-jita ta bata rayuwarta ko ta yi illa ga mutanen da ke kusa da ita ba.