Thursday, April 10
Shadow

Farashin danyen man fetur yayi faduwar da ba’a taba gani ba tun shekarar 2021

Rahotanni daga kasuwar danyen man fetur ta Duniya sun bayyana cewa, Man fetur din yayi faduwar da ba’a taba ganin irin ta ba tun shekarar 2021.

A yanzu ana sayar da gangar danyen man fetur din akan dala $65 kan kowace ganga.

Wanda a baya kamin faduwar wannan farashin, ana sayar da itane akan dala $69.90 kan kowace ganga.

Rabon da aka ga irin wannan faduwar farashin danyen man fetur din, tun shekarar 2021.

Saidai wannan labari zai iya zuwarma da mutanen Najeriya a matsayin me dadi dan kuwa ana sa ran hakan zai sa farashin kayan abinci ya sauka, hakanan farashin man fetur da ake saye shima ya sauka.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda aka kama wata me sayar da abinci na fitsari a cikin tukunyar miyar abincin da take sayarwa

An samu faduwar farashin man fetur dinne dalilin harajin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kakabawa kasashen Duniya.

Hakanan shawarar da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, OPEC suka yanke na kara yawan man fetur din da suke fitarwa zuwa ganga 410,000 shima ya taimakawa farashin faduwa.

Tuni dai masu Deport inda ake saro man fetur din suka rage farashin man inda suma ‘yan kasuwa da masu ababen hawa ke shirin rage nasu farashin.

Saidai hakan zai sa Gwamnatin tarayya ta samu raguwar kudin shiga da take samu ta hanyar sayar da danyen man fetur a kasuwar Duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *