
Rahotanni sun ce Laiyukan ababen hawa sun fara yawa a gidajen Man fetur a sassa daban-daban na Najeriya a yayin da ake fama da hauhawar farashin man a garuruwa daban-daban.
Rahoton yace Farashin litar man fetur din ya kai Naira 1000.
‘Yan kasuwar man fetur sun zargi Depot dake sayar musu man a farashin sari da cewa, sune suka sa man yayi tsada dan sun kara farashin da suke sayar musu da man.
Hakan na zuwane duk da ga matatar man fetur ta Dangote a Najeriya kuma ya fara kai man fetur din zuwa wasu gidajen man kyauta ba kudin dako.