Monday, December 16
Shadow

Farashin Man fetur ya sauka

Farashin daukar man fetur daga inda ake kawo shi a Najeriya ya ragu sosai inda ya samu ragowar kaso 20.34 cikin 100.

Man a yanzu ana daukarsa akan farashin 971.57 kan kowace lita.

Da alama hakan zai kawo sauki sosai a Najeriya lura da cewa tashi ko saukar farashin man fetur din na taba abubuwan amfani da yawa.

Saidai abin mamaki, duk da raguwar farashin, a bangaren ‘yan kasuwa masu sayarwa da mutane a gidanjen man fetur farashin karuwa yayi.

An dai samu karuwar Naira 443 ko ace kaso 79.71 cikin 100.

Daga Naira 617 zuwa Naira 1,060.

Rahoton jaridar Punchng ya nuna cewa a watan Augusta da ya gabata an shigo da man fetur din akan Naira 1,219 amma a watan Nuwamba an shigo dashi akan farashin N971.5.

Karanta Wannan  Muna yin bakin ƙoƙarinmu kan matsalar tsaro - Gwamnatin Sokoto

Saidai duk da haka maimakon farashin man fetur din ya ragu sai ma karuwa yayi.

Rahoton dai ya bayyana dalilin hakan da cire hannun da gwamnati ta yi akan kasuwar man fetur din da kuma tashi da saukar farashin dala a kasuwar Canji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *