
Farfesa Sheriff Muhammad Ibrahim ya bayyana cewa Fulani makiyaya sun shiga gonar shinkafarsa sun cinye masa ita.
Ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook inda da yawa suka jajanta masa.
Ga sakonsa kamar haka:
Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun
Dukkan mai bibiyata ya san irin kokarin da nake yi wajen aikin noma, mun yi duk abunda ya dace kuma gona ta yi kyau sosai, duk da cewa dagangan Gomnati ke karya manoma, hakan bai hana mu dage aikin aikin mu ba. Sai kuma yau na wayi gari da mummunan labarin cewa makiyaya sun cinye mun gona.
Bara ma haka suka yi, suka jawo mun hasara mai yawa, na yi magana suka ce bana son zaman lafiya, ga shi ba na sun saka shanun su sun cinye mun gona ta cikin dare da garken shanu kusan 500.
Lallai ina cikin ma su kwadaitar da mutane su yi noma, amma in dai wannan masifar za ta ci gaba da faruwa, ka noma wani jahilin da bai san halal da haram ba ya zo ya cinye, to ina gari ni dai kam daga bana zan hakura.