Saturday, November 15
Shadow

Bincike ya samu Ministan kimiyya na Najeriya da ‘mallakar takardun boge’

Wani bincike da jaridar Premium Times ta yi ya nuna cewa ana zargin ministan kimiyya da fasaha na Najeriya, Uche Nnaji, da yin takardun kammala karatu na boge, lamarin da ke ci-gaba da janyo cece-kuce a ƙasar.

Binciken da jaridar ta Premium times ta wallafa ya ce an gano cewa ministan ya miƙa takardun bogin ga majalisar dattawan ƙasar domin tattance shi, bayan shugaban Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunansa cikin waɗanda yake so ya bai wa muƙamin minista a shekarar 2023.

Jaridar ta yi ikirarin cewa takardun shaidar kammala karatun digiri da na bautar ƙasa na Mr Nnaji duka na boge ne.

Karanta Wannan  Wasu na ta tambayar wai Ina Kwankwasone, kowane babban dan Adawa yayi Allah wadai da dakatar a Gwamnan Rivers amma har yanzu shi bai ce komai akai ba

Inda ta ƙara da cewa masu suka sun ce ministan bai kammala karatun digirin ba, haka kuma takardar shaidar bautar ƙasar da ya miƙa wa ofishin sakataran gwamnatin tarayya da hukumar tattara bayanan sirri ta DSS da kuma majalisar dattawan na bogi ne.

Kuma binciken da ta yi ya tabbatar mata da cewa takardun na boge ne.

A cewar jaridar a ranar Lahadi ministan ya amince cewa jami’ar Nsukka da ke Najeriyar ba ta taɓa ba shi shaidar kammala karatu na digiri ba.

Batun zargin takardun bogin na cikin manyan batutuwan da suka fi jan hankali a kafafen sada zumunta na Najeriya a ranar Litinin.

Karanta Wannan  Hukumar Kwastam a Najeriya ta kama Kwantena cike da Zqrmalùlun jakai har guda dubu goma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *