
GA WANI DARASI DA YA FARU YAU: Wannan hoton wani iyali kenan da suka yi bankwana da kasar India da nufin za su je cika burinsu na komawa kasar Ingila da zama ashe ajali ke kiransu
A Yau ta ruwaito bayanai sun nuna mijin mai suna Pratik Joshi kwarren mai masanin kwamfuta ne wanda ya dade yana mafarki kwashe iyalansa su koma Ingila da zama. Sannan matarsa sunan ta Dr. Komi Vyas wacce ta ajiye aikinta tayi bankwana da da su akan mafarkinta na komawa Ingaila da zama ya tabbata….
Kwatsam yau sun hau jirgin sama har suka yi wannan hoto suka tura wa dangi a matsayin bankwana sun bar kasa sai jirginsu kirar Air India Flight 171 ya yi hatsari kuma kusan duka fasinjoji fiye da 200 dake jirgin suka mutu
Allah sarki rayuwa ashe duniyar ma za su bari!
Allah ya jikan mamatanmu!