
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya bayyana cewa, gaf yake da barin jam’iyyar APC saboda ba lallai jam’iyyar ta kai labari ba a zaben 2027.
Ndume a wata hira da aka yi dashi a Arise TV yace a baya yayi imanin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai iya gayara matsalolin Najeriya amma daga baya abubuwa suka canja.
Ya bayyana cewa, maganar gaskiya shi tuni ma ya fara halartat tarukan hadakar ‘yan Adawa dan kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027.
Yace amma har yanzu bai yankewa shugaban kasar tsammanin yin gyara ba amma idan aka ci gaba a haka, shi zai fice daga jam’iyyar.