Sunday, November 16
Shadow

Mutane Miliyan 1.3 ne suke mutuwa duk shekara saboda shakar hayakin taba duk da su ba mashaya tabar bane

Rahotan hukumar lafiya ta Duniya, WHO yace mutane Miliyan 1.3 ne ke mutuwa duk shekara daga shakar hayakin taba sigari duk da su ba mashaya tabar bane.

WHO ta fitar da rahoton ne bayan taronta a Birnin Dublin.

Rahoton yace akwai bukatar a samar da tsari da zai dakatar da irin wannan asara da ake yi.

Hukumar ta fito da wani tsari me suna MPOWER wanda tace idan aka bishi za’a samu saukin mutuwar mutane dalilin shan taba Sigari.

Tsarin na dauke da kula da masu shan taba sigari da kuma tsaftace iska da kuma taimakawa masu shan tabar su daina sha.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda Sheikh Salihu Zariya ke cewa, idan Peter Obi ba Alheri bane, Allah ya dauki ransa kamin zabe, a gaban Peter Obin, da yawa dai sun ce dan siyasar be san abinda malam ke cewa ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *