
Dattijon jihar Kano, Dr. Tanko Yakasai ya bayyana cewa, gamayyar su Atiku Abubakar, Peter Obi, da Nasir Ahmad El-Rufai ba zasu yi nasara ba akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ya bayyana hakane a hirar da yayi da ‘yan Jarida a Abuja.
Yakasai wanda shine shugaban kungiyar magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yace babu wanda zai yadda da su Atiku.
Yace saboda a shekarun baya an basu dama su gyara Najeriya amma suka kasa.
Yace a lokacinsu ne aka kashe dala Biliyan $16 dan gyaran wutar lantarkin Najeriya amma bata gyaru ba, sannan yace a lokacinsu ne aka yi badakalar Halliburton har aka daure dan majalisa daga kasar Amurka, amma a Najeriya ba’a daure wadanda suka aikata laifin dashi ba.
Yace maimakon su Atiku su zo su hada kai da Tinubu da yazo gyaran wadancan kura-kurai da suka tafka, amma sai auke hadaka dan kara kwace mulki daga hannunsa.