Monday, December 15
Shadow

Kuma Dai: An sake kama dan daudu Bobrisky, Kalli Bidiyon yanda aka fizgoshi daga kan jirgin sama har ya ji ciwo

Hukumar shige da fici ta kasa ta kama dan daudu, Bobrisky a yayin da yake shirin barin Najeriya.

An kamashine a filin jirgin sama a yayin da yake shirin hawa jirgin sama na KLM zuwa Amsterdam.

Ya bayyana cewa an ji masa ciwo yayin kamen sannan ya zargi cewa hukumar EFCC ce ke da hannu wajan kamun nasa.

Hakanan an ga Bidiyon yanda aka janyoshi daga kan jirgin da karfin tsiya zuwa waje inda da yawa ke tambayar yaya aka yi ya wuce jami’an tsaro ba tare da ganeshi ba.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Dangantaka tsakanin Amurka da Israyla na kara tsami, yanzu haka mataimakin shugaban kasar Amurka, JD. Vance ya soke ziyarar da yake shirin kaiwa kasar saboda rashin jin dadin fadada hàrè-hàrèn da Israyla ke kaiwa Gàzà

Wasu dai sun soki yanda aka kamashi inda suke tambayar laifin me ya aikata inda wasu ke cewa an yi daidai kamun da aka masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *